Lafiya

COVID-19 na ci gaba da raba miliyoyin mutane da guraben ayyukansu

Kasashen Duniya dake fama da cutar Coronavirus
Kasashen Duniya dake fama da cutar Coronavirus DNA India

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa, annobar coronavirus na ci gaba da raba miliyoyin mutane da guraben ayyukansu a sassan duniya, yayin da wasu ma’aikatan ke fuskantar karancin kudaden shiga.

Talla

A wani sabon rahoto da ta fitar, Hukumar Kwadago ta Majalisar Dinkin Duniya ta gano cewa, tsawon sa’o’in aiki ya ragu da kashi 17.3 a cikin tsakiyar wannan shekara a sassan duniya, idan aka kwatanta da watan Disamban bara, abin da ke nufin cewa, kusan mutane miliyan 500 suka rasa ayyukansu.

Wannan adadin ya zarce alkaluman da aka yi hasashe a can baya, na cewa, kimanin mutane miliyan 400 ne za su rasa ayyukansu a dalilin cutar coronavirus.

Shugaban Hukumar Kwadago ta Duniya Guy Ryder ya bayyana lamarin a matsayin musiba, yana mai cewa, kudaden da ‘yan kwadago ke samu a sassan duniya ya ragu da kashi 10.7 a cikin watanni tara na farkon wannan shekara, idan aka kwatanta da bara.

Rguwar kudaden shigar na ‘yan kwadago na nufin cewa, an yi asarar kimanin Dala tiriliyan 3.5 ko kuma an samu raguwar kashi 5.5 na ma’aunin tattalin arziki na GDP.

Annobar coronavirus ta tilasta wa kasashen duniya daukar matakin hana zirga-zirga tare da kulle mutane. gidajensu, lamarin da ya yi mummunar illa ga tattalin arzikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.