Najeriya

Gwamnatin Najeriya za ta yi gyaran dokoki da suka jibanci ruwa a kasar

Daya daga cikin matan dake jan ruwa a wani kauye
Daya daga cikin matan dake jan ruwa a wani kauye ISSOUF SANOGO / AFP

Gwamnatin Najeriya ta shaida cewan babu gudu ba ja da baya kan batun gyaran dokokin albarkatun ruwa na kasar,lamarin da yayi matukar janyo cecekuce musamman a batun sashen da jama’a ke ganin zai musguna musu.

Talla

Ministan yada labarai na Najeriya Lai Mohammed ya shaida cewan babu wani sabon lamari dangane da gyaran dokokin albarkatun ruwa na kasar, kuma abune da ya dauki tsawon lokaci ana batun sa,kawai gyaran fuska ne akeyi don su dace da zamani kamar dai ya da zaku ji a wannan rahoto da Muhammad Sani wakilin mu daga Abuja ya aiko mana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI