RFI tayi Allah wadai da cin zarafin wakilinta a Kamaru

Logon RFI
Logon RFI RFI

Kungiyar dake kare ‘yancin ‘yan jaridun gidan radiyon Faransa International ta yi Allah wadai da babbar murya dangane da cin zarafin da ‘yan sandan Kamaru suka yiwa abokin aikinmu, wakilin sashin Faransancin na RFI dake birnin Yaounde Polycarpe Essomba.

Talla

‘Yan sandan Kamaru dai sunyi ta jibgar dan jaridar na RFI Polycarpe Essomba suna kuma harbin sa da kafa kafin su kuma tsare shi na wani dan lokaci a ofishinsu, sakamakon gudanar da aikinsa na dan jarida yayin zanga-zangar adawa da gwamnatin shugaba Paul Biya da ‘yan adawa suka kira jiya Talata.

Radio France International wanda tace tana goyan bayan wakilinta dari-bisa-dari tayi tir da matakin gwamnatin Kamaru da ta kira na tauye yancin fadin albarkacin baki ne, da kuma hana ‘yan jaridu gudanar da aikinsu.

Kungiyoyin kare ‘yancin ‘yan jaridu na Duniya irinsu Reporters Without Borders da CPJ na kallon Kamaru a matsayin kasar da ke gallazawa ‘yan jaridun dake gudanar da aikinsu tare da tsare su a gidajen kurkuku, kamar yadda tayiwa abokin aikinmu Ahmed Abba, a wasu lokutan ma har da kissa, wanda aka gani kan dan jarida Samuel Wazizi.

CPJ tace an kama wasu ‘yan jaridu 4 a zanga-zangar ta jiya a Yaounde babban birnin kasar da kuma Douala cibiyar kasuwancinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.