Duniya

Ta'addanci da haramtaccen kasuwanci sun addabi Afrika - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Carlo Allegri

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana damuwa kan yadda haramtaccen kasuwanci da cinikin kanana da manyan makamai suka mamaye nahiyar Afirka, inda ya bukaci kasashen duniya da su tashi tsaye wajen ganin sun shawo kan wadannan matsaloli domin hana tashe tashen hankula da ayyukan ta’addancin da ake samu.

Talla

Shugaba Muhammadu Buhari yace yawan hare haren ta’addancin da ake gani yau a duniya na tabbatar da wannan korafi da yake, musamman ganin yadda matsalar ayyukan ta’addanci suka addabi Najeriya, sakamakon rikicin Boko Haram da ‘yan bindiga da ke kai hare hare.

Buhari yace wannan ya tilastawa kasar hadin kai da makotanta wajen yaki da ‘yan ta’adda musamman a Yankin Tafkin Chadi da kuma Sahel baki daya, yayin da yake jaddada matsayin gwamnatinsa na sake gina Yankin Arewa maso gabashin kasar da rikicin Boko Haram ya yiwa illa, da kuma sake tsugunar da mutanen yankin.

Dangane da karfafawa mata gwuiwa wajen ganin sun yi gogayya da maza kuwa, shugaban ya bayyana farin cikinsa da kudirin da ya biyo bayan taron Beijing, yayin da yace kasar za ta cigaba da baiwa mata damar taka rawar da ta dace da su, musamman basu ilimin da ya dace wanda zai taimaka musu.

Shugaban yace wannan ya sa Najeriya za ta dauki nauyin taron duniya karo na 4 wajen tabbatar da samar da ilimi cikin tsaro da kwanciyar hankali a shekara mai zuwa.

Buhari ya kuma sake bayyana muhimmancin baiwa kowanne bangare damar fada aji a Majalisar Dinkin Duniya wajen fadada kwamitin sulhu da kuma baiwa Afirka kujerar din-din-din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI