Najeriya-Kano-Maradi

Najeriya za ta shimfida titin jirgin kasa daga Kano zuwa Maradi

Wani Jirgin kasa
Wani Jirgin kasa RFI / Stéphane Geneste

Gwamnatin Najeriya ta amince da shirin gina hanyar jirgin kasa da zai tashi daga Kano zuwa Maradi a Jamhuriyar Nijar a kan kudin da ya kai Dala kusan biliyan 2.

Talla

Ministan sufuri Rotimi Amaechi ya ce hanyar wadda zata ratsa ta Katsina da Jibiya, zata kuma koma birnin Dutse dake Jihar Jigawa.

Amaechi yace tsayin hanyar zai kai kilomita 248 kuma zata ratsa mazabun Yan Majalisun Dattawa guda 7 in ya tashi daga Kano zai bi ta Dambatta da Kazaure da Daura da Mashi da Katsina da Jibiya zuwa Maradi.

Tun daga shekarar 2018 aka shirya bada wannan kwangilar amma hakan bai samu ba sai a wannan lokaci.

Sufurin jiragen kasa ya taka gagarumar rawa wajen safarar kayayyaki da mutane a shekarun da suka gabata kafin kamfanin ya durkushe a Najeriya.

Yunkurin gwamnatocin da suka gabata, musamman gwamnatin Janar Sani Abacha da Olusegun Obasanjo na farfado da jiragen yaci tura, kafin zuwan gwamnatin Goodluck Jonathan wadda ta gina sabuwar hanyar sufurin daga Abuja zuwa Kaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.