Kamaru

'Yan adawa sun yi tir da gwamnatin Kamaru kan murkushe masu zanga-zanga

Masu zanga zanga a Kamaru.
Masu zanga zanga a Kamaru. AFP Photo/Reinnier Kaze

Jam’iyyar adawa ta MRC a Kamaru tayi tir da matakin gwamnati na baza jami’an tsaro don hanata zanga-zangar ranar 22 ga watan Satumba da ta kira, tare da nuna damuwa kan magoya bayanta da aka kama da kuma ‘yan jaridu.

Talla

Sai dai gwamnati ta kare matakin nata da cewar, ya zama dole ta dauka don tabbatar da doka da oda saboda zanga-zangar haramtacciya ce.

Bayaga neman zaman lafiya a yankunan masu amfani da turancin Ingilishi, karin dalilin da ya sanya ‘yan adawar Kamaru shirya fita zanga-zangar kin jinin gwamnati shi ne yiwa dokokin zaben kasar kwaskwarima.

Ahmad Abba ya hada rahoto kan halin da ake ciki a kasar ta Kamaru, da ya kunshi tsokacin hukumomi a ciki dawajen nahiyar Afrika.

Rahoto kan makomar zanga-zangar adawa da gwamnatin Kamaru

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.