Mali

An rantsar da shugaban rikon kwaryar Mali

Bah Ndaw Shugaban rikon kwariyar Mali a Bamako
Bah Ndaw Shugaban rikon kwariyar Mali a Bamako Michele Cattani / AFP

A yau aka rantsar da shugaban wucin gadin kasar Mali Bah Ndaw, Shugaban kasar da ya rike mukamin Ministan tsaron Mali ,ya kuma rike mukamin dogarin tsohon Shugaban kasar Moussa Traore .

Talla

Wata kusan daya da juyin mulkin da ya kawo karshen shugabancin Ibrahim Boubacar Keita,sabon shugaban ya sabi rantsuwar kama aiki,inda ya bayyana burin san a kawo sauyi don inganta rayuwar yan kasar ta Mali.

Tsohon ministan tsaron na Mali Bah Ndaw da ya taba rike mukamin dogarin tsohon shugaban kasar ta Mali Moussa Traore da ya mutu a makon da ya gabata yana da shekaru 83.

Gabanin hambarar da gwamnatin Ibrahim Boubacar keita a watan Agustan da ya gbata ne, Ndaw ke matsayin ministan tsaro, wanda kuma ya samu horo na musamman a tsohuwar tarayyar Soviet baya ga makarantar horar da Soji da Ecole de Guerre a Faransa.

Sanarwar ta nadin Ndaw na zuwa ne bayan dogon taron da kwamitin da aka dorawa alhakin zabar shugaban ya gudanar, haka zalika zaben na zuwa bayan kungiyar ECOWAS ta bai wa sojin wa’adin kwanaki kan su gaggauta nadin farar hula ko kuma su fuskantar karin takunkumai.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.