Guinea

'Yan adawa na tuhumar shugaban Guinea da shirin haddasa rikicin kabilanci

Shugaban kasar Guniea Alpha Conde
Shugaban kasar Guniea Alpha Conde REUTERS/Afolabi Sotunde/File Photo

Shugaban ‘yan adawa a Guinea Cellou Diallo ya zargi shugaba Alpha Conde da amfani da kabilanci wajen raba kan al’ummar kasar, abinda yace zai iya haifar da yakin basasa.

Talla

Yayin da yake ganawa da manema labarai a Dakar, Diallo yace Guinea za ta gamu da koma baya wajen samun tashin hankalin da zai jefa ta cikin rikicin kabilanci, muddin aka cigaba da sanya batun kabilanci cikin harkokin siyasa.

Yayin jawabi a karshen mako, shugaba Conde yayi amfani da harshen Malinke wajen kira ga ‘yan kabilarsa da su kaucewa zaben dan kabilar Malinke, abinda ya haifar da fargabar barkewar rikicin kabilanci.

A baya bayan Masu sa ido na fargabar barkewar kazamin rikicin siyasar da na kabilancin a kasar ta Guinea tun bayan da shugaba Conde ya sauya kundin tsarin mulki domin yin wa’adi na 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.