Mali

Ana tsare da mawaki Sidiki Diabate a Mali

Mawaki Sidiki Diabaté dan kasar Mali
Mawaki Sidiki Diabaté dan kasar Mali RFI/Claire Bargelès

A yau asabar duban masu kare rajin hakokin mata tareda hadin gwiwar wasu kungiyoyi a Mali ne suka gudanar da zanga-zanga don nuna goyan baya ga tsofuwar mai dakin fittacen mawakin kasar Sidiki Diabate,dake tsare yanzu haka bayan samun sa da laifi dukar tsofuwar matar sa.

Talla

Mawakin dake tsare yanzu haka tun ranar 21 ga wannan watan da muke cikin sa ,ta bakin lauyan sa ana kokarin bata masa suna ne.

Yanzu haka duban masu zanga-zanga ne suka bukaci gwamnati dake ci a Mali yanzu haka da ta dau mataki tareda aiwatar da sabuwar doka don hukunta masu aikata irin wadanan laifuka saman matan su tareda cin zarafin su a duk inda suke cikin kasar.

Yanzu haka da dama daga cikin kamfanoni da suka kulla yarjejeniya da fittacen mawakin kasar ta Mali Sidiki Diabate ,irin su Universal Music Africa sun sanar da yanke duk wata hulda da shi biyo bayan tsare da ake yi yanzu haka a kurkuku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI