Chadi

Dakarun Chadi sun halaka mayakan Boko Haram 20

Wasu dakarun sojin kasar Chadi.
Wasu dakarun sojin kasar Chadi. Reuters

Sojin Chadi sun halaka mayakan Boko Haram 20 tare da ceto fararen hula 12 da mayakan suka yi garkuwa da su, ciki har da kananan 9.

Talla

Ministan yada labaran Chadi Sharif Mahamat Zene ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar ranar 17 ga Satumban da muke mayakan Boko Haram suka kaiwa wani kauye dake yankin Tafkin Chadi farmaki, inda suka sace mutanen.

Sai dai bayan farautar su, sojin na Chadi suka samu nasarar halaka 15 daga cikin mayakan a garin Barkalam da ke gaf da iyakar Najeriya.

Cikin watan Afrilu, biyo bayan kashe sojin Chadi akalla 100 da mayakan Boko Haram suka yi ne, sojojin suka kaddamar da gagarumin farmaki kan kungiyar a karkashin jagorancin shugaban kasar Idriss Deby, wanda yayi shelar kawo karshen su, bayan halaka mayakan dubu da yace sun samu nasarar yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.