Ivory Coast

Gbagbo na da 'yancin sake neman shugabancin Ivory Coast - Kotu

Tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo.
Tsohon shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo. Jerry Lampen/Pool via REUTERS

Kotun kare hakkin dan adam ta nahiyar Afrika ta umarci gwamnatin Ivory Coast da ta baiwa tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo damar tsayawa takara a zaben shugabancin kasar da ke tafe a watan Oktoba.

Talla

Yayin yanke hukuncin a ranar Juma’a, kotun ta baiwa gwamnatin kasar ta Ivory Coast umarnin gaggauta kawar da dukkanin shingayen da suka haramtawa tsohon shugaba Gbagbo sake tsayawa takara.

Kimanin watanni 2 baya, kotun kolin Ivory Coast ta yi watsi da takarar mutane 40 daga cikin 44 da ke neman kujerar shugabancin kasar a zaben da ke tafe, cikinsu har da tsohon shugaba Laurent Gbagbo da tsohon madugun ‘yan tawaye Guillaume soro, wadanda dukkaninsu suka taka rawa a rikicin siyasar da ya lakume rayuka akalla dubu 3 cikin shekarar 2010.

Sai dai babbar kotun ta Ivory Coast ta amince da takarar Alassane Ouattara dake neman wa’adi na 3, duk fuskantar caccakar da yake na sabawa kundin tsarin mulkin kasar da ya kayyade wa’adin shugabanci 2.

A hain yanzu dai lokaci ne kawai zai fayyace ko gwamnatin kasar ta Ivory Coast za ta bi umarnin kotun kare hakkin dan adam ta Afrika, la’akari da cewar cikin watan Afrilun wannan shekara ta 2020, kasar ta fice daga karkashin kotun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.