Afrika

Najeriya ta sanar da rufe wasu wurare da ake killace masu dauke da Corona

Jami'an kiwon lafiya dake gudanar da gwajin kan marasa lafiya
Jami'an kiwon lafiya dake gudanar da gwajin kan marasa lafiya REUTERS

Gwamnatin Najeriya ta rufe wurare biyu da aka ware domin killace masu fama da cutar korona saboda raguwar masu dauke da cutar a birnin Abuja.

Talla

Hukumomin kasar sun ce an rufe wuraren biyu dake Karu da Asokoro, yayin da wadanda ke Idu da THISDAY zasu cigaba da zama a bude domin karbar marasa lafiyar.

Rahotanni sun ce an samu gagarumar nasara wajen rage yawan masu harbuwa da cutar, inda ake samun mutane kasa da 300 dake kamuwa da cutar kowacce rana a Najeriya, sabanin yadda aka saba gani.

Ya zuwa yanzu mutane sama da 58,000 suka kamu da cutar a Najeriya, kuma 49,000 sun warke, yayin da sama da 1,100 suka mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.