Mali

Shugaban rikon kwaryar Mali ya yabawa Ecowas

Bah N'Daw shugaban rikon kwaryar Mali da mataimakin sa
Bah N'Daw shugaban rikon kwaryar Mali da mataimakin sa REUTERS/Amadou Keita

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar Mali Bah N’daw ya yabawa kungiyar kasashen Afirka ta Yamma da kuma Jakadanta na musamma kuma tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kan rawar da suka taka wajen wanzar da kwanciyar hankali a kasar bayan matsalolin da aka samu.

Talla

N’daw wanda aka rantsar da shi domin jagorancin gwamnatin da zata shirya zabe a kasar yace shugaba Jonathan ya taka gagarumar rawa wajen baiwa jama’ar kasar kwarin gwuiwar samo hanyar warware matsalolin da suka addabe su.

Ana saran kungiyar ECOWAS ta cirewa kasar takunkumin karya tattalin arzikin da ta dora mata muddin kasar ta nada Firaminista farar hula da kuma sakin sauran jami’an gwamnatin da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.