Najeriya-Sokoto

Dan sandan Najeriya ya bude wuta a Masallacin Juma'a

Wasu 'yan sandan Najeriya.
Wasu 'yan sandan Najeriya. AFP

Rundunar Yan Sandan Najeriya dake Jihar Sokoto ta kama wani jami’in ta da ake kira Saje Bello Garba saboda yadda ya bude wuta a Masallachin Juma’ar Sultan Muhammadu Bello inda ya kasha mutuum guda, ya kuma raunata wasu guda 3.

Talla

Rahotanni sun ce jami’in Yan Sandan dake kokarin kare manyan baki da suka hada da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ya bude wuta ne lokacin da matasa ke kokawar karbar kudin da gwamna Tambuwal ya basu bayan sallar juma’a.

Kakakin rundunar Yan Sandan Jihar Muhammad Sadiq yace kwamishinan Yan Sanda Ibrahim Sani Kaoje ya bukaci sashen binciken Yan Sanda ya gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.

Kwamishina Kaoje ya bayyana damuwa kan nuna rashin kwarewar aiki da jami’in yayi, bayan ya bada umurnin a tsare shi, yayin da ya gargadi jami’an sa da su dinga aiwatar da aikin su kamar yadda doka ta tanada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.