WHO-Afrika

Yanayin zafi da yawan matasa sun hana coronavirus yin muni a Afrika - WHO

Adadin masu kamuwa da cutar coronavirus a Afrika na cigaba da raguwa a tsawon watanni 2.
Adadin masu kamuwa da cutar coronavirus a Afrika na cigaba da raguwa a tsawon watanni 2. Reuters

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce Afrika ta tsira daga fuskantar bala’in karuwar mutanen da a baya kwararru suka yi hasashen za su harbu da annobar coronavirus gami da rasa rayukansu a nahiyar.

Talla

WHO ta bayyana yawan matasa masu lafiya, da kuma yanayin zafi a matsayin wasu daga cikin muhimman dalilan da suka taimakawa nahiyar ta Afrika.

Hukumar lafiyar ta ce kawo yanzu akalla mutane dubu 34 da 706 annobar ta coronavirus ta halaka a Afrikan daga cikin akalla miliyan 1 da dubu 439 da suka kamu da cutar, ta’adin da ko kusa bai kai wadda annobar ta yi a wasu nahiyoyin ba, inda a Amurka kadai cutar ta lakume rayuka akalla dubu 202, daga cikin mutane kusan miliyan 7 da suka kamu.

Sabbin alkaluman da WHO sun kuma ce karfin yaduwar annobar ta COVID-19 ya ragu matuka a taswon watanni 2 a kasashen da a baya cutar tafi karfi cikinsu da suka hada da Algeria Habasha, Najeriya, Afrika ta Kudu da kuma Ghana.

Hukumar lafiyar tace a tsawon makwanni 4 na baya bayan nan, mutane dubu 77 da 147 ne suka kamu da cutar ta COVID-19, sabanin dubu 131 da suka kamu a makamancin lokacin na makwanni 4.

A halin yanzu annobar coronavirus a Afrika tafi muni a Afrika ta Kudu, inda akalla mutane dubu 667 suka kamu da cutar, daga cikinsu kuma dubu 16 da 283 suka halaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.