Najeriya

ACF ta zargi jami'an Najeriya da kaiwa Zulum hari

Gwamnan jihar Borno a Najeriya yayin ziyarar da ya kai Magumeri bayan harin Boko Haram.
Gwamnan jihar Borno a Najeriya yayin ziyarar da ya kai Magumeri bayan harin Boko Haram. RFI Hausa

Kungiyar Yan Arewacin Najeriya ta ACF ta bayyana matukar kaduwar ta da harin da aka kaiwa tawagar Gwamnan Jihar Barno Babagana Zulum lokacin da ya kai ziyarar aiki a Baga domin sake tsugunar da ‘Yan gudun hijirar da suka koma gidajen su, inda take cewa muddin wani abu ya samu gwamnan ba zai yiwa Najeriya kyau ba.

Talla

Sanarwar da kungiyar ta gabatar na cewa akwai tambayoyi da dama da ya dace gwamnati da jami’an sojojin Najeriya su amsa kan wannan hari wanda ke dada zubar da kimar su wajen yaki da ‘yan ta’adda.

Sanarwar da kakakin kungiyar Emmanuel Yawe ya rabawa manema labarai ta koka kan yadda bangarorin biyu suka gaza wajen tabbatarwa jama’a alkawarin da suka yi na murkushe Yan ta’adda wadanda ke cigaba da kashe rayuka.

Yawe yace a makon jiya kawai hare hare sun salwantar da rayukan Yan Sanda 8 da sojoji 3, kwanaki bayan hallaka Kanar Dahiru Bako da jami’an sa a Damboa.

Sanarwar ta bukaci sojojin Najeriya da su gaggauta daukar matakan da zasu kare kimar su a idan jama’a wajen kawo karshen wadannan hare hare, yayin da suka bukaci gwamnati da ta kara kaimi wajen kara kwazon jami’an tsaro.

Kungiyar ACF tayi gargadin cewar muddin wani abu ya samu Gwamna Zulum wanda ke jajircewa wajen yiwa jama’ar sa aiki, abinda zai biyo ba ba zai yiwa Najeriya kyau ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.