Amurka

Trump ya bukaci yiwa Joe Biden gwajin kwaya kafin mahawarar

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. MANDEL NGAN / AFP

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci yiwa abokin takarar sa Joe Biden gwajin kwaya kafin mahawarar da za suyi ranar talata ta talabijin ko kuma bayan kamala mahawarar domin sanin halin da yake ciki.

Talla

A sakon da ya aike ta kafar twitter, Trump yace yana matukar bukatar ganin an yiwa Biden gwajin saboda baiwa jama’a damar sanin yanayin dan takarar.

Trump yace a shirye yake shima a gwada shi, kuma kowa ya san cewar babu wanda zai kara da shi wajen mahawara.

Shugaban ya dade yana zargin Biden cewar yana amfani da kwayar dake kara masa kuzari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.