Burkina Faso

'Yan ta'adda sun halaka jami'an sa kan Burkina Faso sama da 100

Sojin Burkina Faso da na Austria yayin atasaye a gaf da birnin Ouagadougo
Sojin Burkina Faso da na Austria yayin atasaye a gaf da birnin Ouagadougo AFP

Rahotanni daga Burkina Faso sun ce gungun ‘yan bindiga dauke da manyan makamai sun halaka jami’an tsaron sa kai 6, bayan kaiwa kauyen Touldeni da ke gabashin kasar farmaki.

Talla

Jami’an tsaron sa kan na kungiyar VDP na kokarin bin sawun maharan ne, bayan farmakin da suka kai a Juma’ar da ta gabata, lokacin suka gamu da ajalinsu.

Kididdiga a baya bayan nan ta nuna cewar kawo yanzu sama da ‘yan sa kan kungiyar ta VDP 100 ‘yan ta’adda suka halaka a Burkina Faso daga watan Janairun wannan shekara zuwa yanzu.

A watan Nuwamban shekarar bara gwamnatin Burkina Faso ta kafa jami’an tsaron na sa kai, domin taimakawa sojin kasar wajen yakar ‘yan ta’adda, wadanda ake baiwa sabbin dauka horon makwanni 2, kafin basu kananan makamai, don gudanar da sintiri a sassan kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.