ECOWAS-Mali

ECOWAS za ta yi zama na musamman kan Mali bayan nadin Firaminista

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya ke karbar rahoton jakadan ECOWAS a Mali kuma tsohon shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari lokacin da ya ke karbar rahoton jakadan ECOWAS a Mali kuma tsohon shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan. RFI hausa

Shugabannin Kungiyar ECOWAS za su sake gudanar da wani taro domin duba rahotan Jakadan kungiyar Goodluck Jonathan dangane da halin da ake ciki a Mali, bayan nadin Firaminista farar hula da zai jagoranci gwamnatin kasar.

Talla

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana haka, bayan ganawar da suka yi da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan wanda ya yi masa bayani kan irin cigaban da aka samu.

Sai dai Jonathan ya ce har yanzu da sauran ruwa a kaba, ganin yadda sojojin da suka yi juyin mulki suka ki nada mataimakin shugaban kasa farar hula kamar yadda ECOWAS ta bukata.

Buhari ya bukaci Jonathan ya gabatar da rahotan aikin sa ga shugaban Ghana Nana Akufo-Addo da ke shugabancin ECOWAS, domin bashi damar kiran taron kungiyar da zummar yin Nazari akai.

Shugaban Najeriya ya ce a halin da Mali ta ke ciki a yau, da kashi biyu bisa uku na yankin kasar ke hannun 'yan ta’adda, abinda ya kamata sojoji su yi shi ne kwato yankunan maimakon kokawar mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.