Gwamnonin Najeriya sun maka shugaba Buhari kotu

Gwamnonin Najeriya sun maka shugaba Buhari kotu

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. © Nigeria Presidency/Handout via REUTERS

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 sun maka shugaban kasar Muhammadu Buhari a kotun kolin, sakamakon wata dokar da ya sanya wa hannu a watan Mayun wannan shekarar.

Talla

Jihohin sun ce wannan doka da shugaban kasar ya sanya wa hannu ta tura ilahirin nauyin da yake kan gwamnatin tarayyar na gudanar da manya da kananan ayyukan manyan kotunan jihohi da kotunan daukaka kara na Shari’ar Musulunci, da na al’adu zuwa kan jihohi.

Sun kara da cewa in ban da albashin ma’aikatan wadannan kotunan da suka zayyana, shugaba Buhari ya yi watsi da manya da kananan ayyuka na wadannan kotuna tun a wata Mayu.

Masu shigar da karar sun yi zargin cewa dokar da shugaban na Najeriya ya sanya wa hannu ta yi hannun riga da kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 1999, saboda haka suke bukatar kotun kolin ta yi watsi da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.