Afrika-MDD

Kasashen Afrika sun tafka asarar Dala biliyan 836 da aka fitar ketare- MDD

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya alakanta koma bayan da kasashen na Afrika ke fuskanta.
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya alakanta koma bayan da kasashen na Afrika ke fuskanta. AFP Photo/MOHD RASFAN

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kasashen Afirka sun yi asarar kudaden da suka kai Dala biliyan 836 ta hanyar fitar da su zuwa kasashen duniya ta hanyar da ba su kamata ba a cikin shekaru 15.

Talla

Hukumar Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da kasuwanci da kuma cigaba ta gabatar da rahoto akai, inda ta ke cewa kudaden sun zarce Dala biliyan 770 da ake bin nahiyar baki daya a shekarar 2018.

Sakatare Janar na Hukumar Mukhisa Kituyi ya ce halarta kudaden na haramun wajen fitar da su nada nasaba da kayayyakin da ake fakewa da su da suka hada da zinare da lu’u lu’u, daga kudaden da ake sacewa daga lalitar gwamnati ko kuma harajin da aka tara.

Rahotan ya ce wannan satar na matukar illa ga gwamnatocin Afirka wadanda ke matukar bukatar kudaden domin samarwa jama’ar su asibitoci da makarantu da kuam kayan more rayuwa.

Majalisar ta ce cin hanci da rashawa da kuma sace dukiyar kasashe ana fitar su na hana Afirka cigaba wajen janye mata kudaden canjin da ta ke bukata da kuma rage arzikin da nahiyar ke samu tare da dakile kasuwanci da kuma haifar da talauci a cikin al’umma.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.