Najeriya-Kamaru

'Yan awaren Kamaru sun kulla yarjejeniyar hadewa da 'yan Biafra a Najeriya

Wata zanga-zangar kungiyar 'yan Biafra masu fafutukar ballewa daga Najeriya.
Wata zanga-zangar kungiyar 'yan Biafra masu fafutukar ballewa daga Najeriya. AFP Photo/Pius Utomi Ekpei

‘Yan awaren Kamaru sun sanar da kulla yarjejeniyar taimakon juna tsakaninsu da kungiyar matasan Biafra mai rajin ballewa daga Najeriya, a wani yunkuri na tallafawa juna kan fafutukarsu ta samar da kasashe masu cin gashin kansu daga cikin Najeriyar da Kamaru.

Talla

‘Yan awaren biyu daga makwabtan kasashen da suka gudanar da taron kulla yarjejeniyar a karshen makwan da ya gabata, tare da samar da shalkwata ta musamman a Enugu da ke Najeriya sun aminta da taimakawa juna a fafutukarsu, inda jagoran kungiyar matasan Biafran ta BNYL Princewill Chimezie ke cewa kungiyoyin biyu na kamanceceniya da juna dalilin da ya sanyasu taimakekeniya tsawon lokaci amma sai a wannan karon ne suka ga dacewar hadewa don habaka ayyukansu.

Babban taron hadewar da ya samu halartar wakilan ‘yan awaren kamarun da ke fatan kafa jamhuriyyar Ambazonia, Comrade Enow Arrey ya ce kisan da ake yiwa ‘yan uwansa da ke yankin arewa da kuma gabashin kamarun masu amfani da turancin Ingilishi, ya tilasta shi gudun hijira zuwa jihar Cross River a Najeriya, ko da ya ke yanzu ya samu kwarin gwiwar taimakawa wajen tunkarar matsalar tare da maganceta don tabbatuwar kafuwar kasar ta Ambazonia.

A cewar Arrey zamansa a Najeriya ya gano cewa ‘yan Biafran na fuskantar makamanciyr matsalar da ‘yan awaren Kamarun ke fuskanta ta yadda gwamnati ke dakushe kokari da fafautukarsu ta samarwa yankin nasu ‘yanci.

A bangare guda Princewill Chimezie ya bayyana cewa a yanzu lokaci ya yi da za su kare kansu domin babu dalilin da zai sanya su zuba ido su kallo ana yiwa ‘yan uwa da mambobinsu kisan gilla, kuma ta hanyar hadewar ne kadai duniya za ta ji muryarsu tare da kai w aga nasara dangane da shirinsu na kasa kasashe biyu masu cin gashin kansu, da za su balle daga kasashen na Najeriya da Kamaru.

Tun tsakanin 1967 zuwa 1970 aka samar da kungiyar ta ‘yan Biafra karkashin jagorancin Janar Chukwumeka Odumegwu-Ojukwu da ke fafutukar ballewa daga Najeriya wadda t kai ga yakin basasa na tsawon lokaci gabanin dankwafar da kungiyar a wancan lokaci, inda a bangare guda itama Kamaru ke fama da makamanciyar kungiyar ko da yak e sai shekaru 3 da ya gabata ne ta fara rike makami.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.