Rashin azanci ne Najeriya ta sayar da mai kasa da yadda Saudiyya ke sayarwa - Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce rashin azanci ne a ce kasar ta sayar da albarkatun man fetur a farashi kasa da yadda kasashen da ke makwaftaka da ita suke sayarwa.
Wallafawa ranar:
A safiyar Alhamis dinnan ya yi wannan furuci ne a jawabin da ya gabatar na bikin cikar kasar shekaru 60 da samun ‘yancin kai.
Shugaba Buhari ya ce baya ga kalubalen anobar coronavirus, kasar ta fuskanci tabarbarewa a fannin samun kudaden musayar kasashen waje, da ma kudaden shiga daga cikin gida, biyo bayan faduwar da farashin danyen mai ya yi da kashi 40, lamarin da ya haddasa rikitowa na kashi 60 a kudaden da kasar ke samu.
Ya ce kasar na fama da kalubale mai kifi biyu, wanda su ne ceto rayuka da inganta rayuwa a yanayi na tabarbarewar tattalin arziki.
Shugaban Najeriya ya ci gaba da cewa, za a yi wa farashin albarkatun mai a kasar garambawul, indaa yaa ke cewa ana sayar da litar man fetur a kan Naira 161, wanda yayi araha ainun idan aka kwatanta da na kasashen da ke makwaftaka da Najeriya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu