Najeriya

'Yan ta'adda sun kashe dakarun Najeriya 10 a wani kwanton bauna

Motar kungiyar ISWAP da sojin Najeriya suka kwato.
Motar kungiyar ISWAP da sojin Najeriya suka kwato. AUDU MARTE / AFP

Mayaka masu ikrarin jihadi da karfin tsiya na kungiyar ISWAP sun kashe dakarun Najeriya 10 a wani harin kwanton bauna da suka kai masu a yankin Tafkin Chadi dake yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Talla

Dakarun na kungiyar ISIS reshen yammacin Afrika sun kai wa ayarin motocin sojin da ke dauke da kayan abinci hari ne da manyan bidigogi, inda suka kashe sojoji 10, ciki har da hafsoshi 2, yayin da wasu 8 suka ji rauni, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito.

Motocin sojin na kan hanyar su ne dauke da kayan abinci da sauran kayan aiki da za a kai wa sojojin dake bakin daga, a lokacin da harin ya auku.

Maharan sun kona motoci biyu da tare da kwashe kayan abinci kamin su tsere a cikin daji.

Wannan hari ka iya zama na ramuwar gayya, biyo bayan wani samame da sojin Najeriya suka kai, har ma suka tarwatsa maboyar yan bindiga tare da kashe wasu da dama ciki har da manyan kwamandodi biyu.

Kungiyar ta ISWAP ta raba gari da Boko Haram a shekarar 2016.

A ranar juma’ar da ta gabata, mayakan sun kai wa tawagar Gwamna jihar Borno hari a kan hanyarsa ta zuwa Baga

Rikicin Boko Haram da aka fara a 2009 ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 36, a yayin da fiye da mutane miliyan biyu suka bar gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.