Ba zan bari Amurka ta kai wa al-Shabab hari ta kasata ba - Uhuru Kenyatta

Shugaban Amurka  Donald da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta, a birnin Washington.
Shugaban Amurka Donald da takwaransa na Kenya Uhuru Kenyatta, a birnin Washington. NICHOLAS KAMM / AFP

Shugaban Kasar Kenya, Uhuru Kenyatta ya bayyana cewa ba zai baiwa Amurka damar amfani da Kasarsa wajen kaiwa mayakan al-shabab hari da jirage masu sarrafa kansu.

Talla

Shugaban na Kasar Kenya wanda ya kai ziyara Faransa yace kawo yanzu dai bai karba wata bukata daga Amurka ba, na barin jiragen masu sarrafa kansu shiga Kasarsa dan kaiwa mayakan al-shabab hari ba.

Ko da yake a cikin watan da ya gabata ne dai jaridar The New York times ta Kasar Amurka, ta ce wasu majiyoyi daga sojin Amurkan na neman amincewar gwamnatin Kenya don yin amfani da jirage marasa matuka wajen kai wa mayakan na al-Shabab da ke gabashin Kenya hari.

Rahoton na zuwa ne kwanaki kafin kotun soji dake Somalia ta yanke wa wani dan kungiyar IS hukuncin daurin rai da rai bayan kama shi da hannu a wani kazamin hari da aka kai wa sansanin sojin Amurka da ke Kenya. Harin da kungiyar ta kai a karon farko.

Kenya dai na da dakaru akalla dubu 20 a cikin sojojin Kungiyar Kasashen Afrika da ke yakar yan ta’adda a Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.