Jagoran juyin mulkin Mali ya sassauto kan batun maye gurbin shugaban kasa

Bisa dukkan alamu dai jagoran Soja da suka kwace Mulki a kasar Mali Kanar Assimi Goita ya jingine burinsa na maye gurbin shugaban rikon kwaryan kasar idan aka sami laluran laulayin rashin lafiya.

Kanal Assimi Goita, jagoran mulkin Soji a Mali.
Kanal Assimi Goita, jagoran mulkin Soji a Mali. ANNIE RISEMBERG AFP/File
Talla

Karkashin tsarin farko bayan kifar da Gwamnatin farar hula ta Boubakar Keita ranar 18 ga watan Augusta dai, kamar yadda bayanan suka shiga hannun manema labarai, Jagoran sojan ne zai maye gurbin wanda aka nada don shugabantar gwamnatin rikon kwarya idan akwai bukatar haka.

Yanzu haka dai jagoran sojan shine mataimakin shugaban Gwamnatin rikon kwaryar Tsohon Kanar na Soja Bah Ndaw, da zasu Mulki kasar na tsawon watanni 18, kafin a yi zabe.

Shugabannin kungiyar ECOWAS ko CEDEAO na adawa ne da batun Soja ya hau kujeran mulkin kasar.

Wani jami’in Majalisar Dinkin Duniya na cewa watakila ganin an sasanta wannan batu, nan gaba kadan a sassauta takunkumin da aka kirba wa kasar na kyamatar dukkan harkan arziki da ita.

Tun a ranar Alhamis ne dai aka wallafa sabon tsarin da za’a tafiyar da Gwamnatin rikon kwaryar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI