Najeriya: PDP ta bukaci Buhari ya hada kan al’umma

Jam’iyar adawa ta PDP a Najeriya ta shawarci shugaban kasar, Muhammadu Buhari da ya karfafa dabi’ar girmama doka da tabbatar da hadin kan al’umma.

Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus. TWITTER/UcheSecondus
Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya Uche Secondus. TWITTER/UcheSecondus TWITTER/UcheSecondus
Talla

A wata sanarwa da ta samu sa hannun sakataren watsa labaran jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, wadda martani ne ga jawabin shugaba Buhari na ranar bikin cikar kasar shekaru 60 da samun ‘yancin kai, PDP ta bukaaci Buhari da ya dau matakan ganin ana damawa da kowane bangare a harkokin tafiyar da kasar, da kuma tabbatar da ganin babu wani dan Najeriya da zai ji cewar an bar shi a baya a kowane fanni na rayuwa, ba tare da la’akari da addini ko kabila ko bangarensa ba.

Mr Ologbondiyan ya shawarci shugaban na Najeriya da ya dau matakan gaggawa na kawo karshen kalubalen rarrabuwar kawuna, da kuma matsalolin tattalin arziki da suka addabi kasar.

Ya kuma shawarce shi da kada ya yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da an ci gaba da tataunawar da za ta kai al’ummar kasar ga samun albarkatun man fetur a farashi mai rahusa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI