Sudan ta kulla zaman lafiya da 'yan tawaye
Gwamnatin Sudan da Kungiyoyin ‘yan tawayen kasar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya mai cike da tarihi da zummar kawo karshen yakin da aka kwashe gomman shekaru ana fama da shi, lamarin da ya yi sanadiyar salwantar dubban rayukan al’umma.
Wallafawa ranar:
An yi ta guda da shewa a daidai lokacin da wakilan gwamnati da na ‘yan tawayen ke sanya hannu kan wannan yarjejeniya da suka cimma bayan shekara guda da gudanar da tattauna tsakanin bangarorin biyu.
Yarjejeniyar dai ta kunshi abubuwa da dama da suka hada da batun mallakar filaye da biyan kudaden diyya da rarraba madafun iko da kuma mayar da ‘yan gudun hijira matsugunansu.
An gudanar da bikin ne a babban birnin Juba na Sudan ta Kudu kamar yadda daya daga cikin ‘yan jaridun Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya rawaito.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu