Mali ta saki 'yan ta'adda sama da 100 domin ceto jami'an gwamnati da wasu Faransawa

Gwamnatin Mali ta amince da sakin wasu mayakan kungiyoyi masu ikirarin jihadi 100 karkashin yarjejeniyar sako fitattun ‘yan siyasar kasar, ciki har da jagoran ‘yan adawa Souma’ila Cisse da ke tsare a hannun mayakan da kuma jami’ar agajin Faransa da itama aka yi garkuwa da ita.

Dakarun tsaron Mali
Dakarun tsaron Mali MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Majiyoyin masu shiga tsakani sun ce, irin wannan saki ya kasance wani bakon abu da aka gani a kasar ta Mali.

Uwargida Sophie Pétronin da Soumaïla Cissé, na daga cikin mutanen da batun sakin nasu ke kan sikeli, uwargida Sophie Pétronin dai ta kasance bafaransa ta karshe da ake garkuwa da ita a duniya, yayin da Sumaila sise ke zama daya dag cikin manyan shikashikan dake tallafe siyasar kasar ta Mali da mayakan dake ikararin jihadi suka yi garkuwa da shi.

Tattaunawar neman sakin nasu dai, ta haifar da a jiya lahadi sakin daruruwan mayakan jihadi a fadin kasar ta Mali.

Wani jami’in tsaron kasar ta Mali da ya bukci sakaya sunansa saboda girman lamarin ya sanar da AFP cewa, an saki fursunonin da ake tsare da su ne a yankunan Niono dake tsakkiya da kuma Tessalit dake aracin kasar.

Ita dai jami’ ar wata kungiyar tallafawa yara mai zaman kanta bafaransa Sophie Pétronin, yar 75 da haihuwa, wani gungun masu dauke da makamai ne suka sace ta a ranar 24 ga watan December 2016 a garin Gao dake arewacin kasar ta Mali.

Shi kuma Soumaïla Cissé, mai shekaru 70, da ya kasance tsohon pm haka kuma madugun yan adawa a majalisar dokoki, wanda kuma sau uku ya na zuwa na 2 a jere a zabuka shugabancin kasar da aka gudana a Mali, an yi garkuwa da shi ne a ranar 25 ga watan Maris da ya gabata lokacin da yake gudanar da yakin neman zaben yan majalisar dokoki a yankin Tombouctou (arewa maso yammacin kasar ta Mali).

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI