Mali-ECOWAS

ECOWAS ta cire wa Mali takunkumi

ECOWAS ta janye takunkumin ne bayan sojoji sun mutunta wasu sharudda.
ECOWAS ta janye takunkumin ne bayan sojoji sun mutunta wasu sharudda. Nipah Dennis / AFP

Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma ta ECOWAS ta sanar da cire takunkumin karya tattalin arzikin da ta dora wa Mali sakamakon juyin mulkin da soji suka yi a watan Agusta, saboda ci gaban da aka samu wajen nada shugabannin fararen hula da za su jagoranci kasar zuwa zabe.

Talla

Sanarwar da kungiyar ECOWAS ta gabatar ta ce shugabannin kasashen da ke Afrika ta Yamma sun yanke hukuncin cire wa Mali takunkumi saboda ci gaban da aka samu wajen mayar da kasar turbar doka da oda.

Kungiyar ta ce ta gamsu da shirin yadda za a tafiyar da gwamnatin rikon kwaryar kasar da zai kai ga gudanar da zabe da kuma nada shugaban kasa da firaministan fararen hula.

ECOWAS ta bukaci abokan huldarta da hukumomin duniya da su koma hulda da sabuwar gwamnatin Mali sakamakon cire takunkumin, yayin da ta bukaci sakin jami’ai fararen hula da soji da aka tsare bayan juyin mulkin kasar.

Sanarwar ta ECOWAS na zuwa ne kwana guda bayan da shugaban kasa na riko Bah Ndaw ya nada majalisar ministoci a karkashin jagorancin firaminista Moctar Ouane.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI