Mali

Sojoji sun mamaye mukamai a sabuwar gwamnatin Mali

Mali ta sanar da kammala kafa sabuwar gwamnatin rikon kwarya mai kunshe da kaso mai yawa na jami’an Soji da za su rike mukamai daban-daban, gwamnatin da ke zuwa biyo bayan juyin mulkin watan Agusta da ya hambarar da shugaba Ibrahim Boubacar Keita.

Jagororin sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Mali.
Jagororin sabuwar gwamnatin rikon kwarya a Mali. REUTERS/Amadou Keita
Talla

Ma’aikatun da suka kunshi na tsaro, ayyuka na musamman da kuma tsare-tsaren gwamnati baya mai’aikatar da za ta taka rawar shiga tsakani don sasanta rikicin da kasar ke fuskanta da kuma tabbatar da ci gaba, dukkanninsu na karkashin jagorancin jami’an Sojin na Mali yayin da fararen hula ke da mukamai akalla 21 cikin hwamnatin hadin kan.

Yanzu haka dai sabuwar gwamnatin rikon kwaryar ta Mali za ta jagoranci kasar tsawon watanni 18 gabanin mika mulki ga farar hula kamar yadda yarjejeniyar bangarorin biyu ta kunsa bisa bukatar hakan daga kasashen Duniya.

Sai dai babu tabbacin ko ECOWAS za ta amince da da janyewawa kasar takunkuman da ta kakaba mata bayan juyin mulkin na watan Agusta la’akari da cewa gwamnatin hadaka ba ta ginu bisa bukatar kungiyar ba.

Sabuwar gwamnatin wadda Bah Ndaw za ke rike mukamin shugaban kasa Assimi Goita da ya jagoranci juyin mulkin kuma a matsayin mataimaki, Moctor Ouane da ke matsayin Firaminista ne kadai ba jami’in Soji ba a mukamin ‘yan sama-saman sabanin yadda ECOWAS ta bukata, ko da ya ke hatta a gwamnatin Boubacar Keita Soji ke jagorantar kaso mai yawa na bangarorin tafiyar da mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI