Kotun Kenya ta samu wasu mutane 2 da laifin taimakawa kungiyar Al-shebab

Wata kotun Kenya ta samu mutane biyu da laifi saboda rawar da suka taka a wani hari da aka kaddamar kan rukunin shagunan Westgate da ke birnin Nairobi na Kenya a shekarar 2013, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 67.

Sojojin Kenya a kan iyakar kasar da Somalia
Sojojin Kenya a kan iyakar kasar da Somalia AFP
Talla

Tun a cikin watan Janairun shekarar 2014 aka fara zaman shari’a , yayin da a yau Laraba, alkalin kotun Majistire Francis Andayi ya samu Mohd. Ahmed Abdi da kuma Hassan Hussein Mustafa da hannu a harin, ganin yadda suka taimakawa maharan kaddamar da farmakin wanda kungiyar Al-Shebab ta dauki alhakinsa.

Sai dai kotun ta wanke mutun guda wato Liban Abdullahi Omar daga dukkan zarge-zargen da ake yi masa , kuma nan take ta ba shi umarnin ficewa daga harabar koton.

Sai din kawo yanzu, babu cikakken bayani kan ko kotun za ta yanke hukunci cikin hanzari kan masu laifin ko kuma za ta jinkirta har zuwa wani lokaci nan gaba.

Alkalin kotun ya ce, mutanen biyu sun yi ta ganawa ta wayar tarho da maharan akai-akai , abi da ke nuna cewa, alakarsu ta wuce ta abokai.

Kodayake babu wata takamammiyar shaidar da ke nuna cewa, mutanen biyu sun bada tallafin makamai ga wadannan mahara da tuni aka hallaka su a yayin garkuwa da jama’a a lokacin farmakin na Westgate.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI