Gwamnatin rikon kwaryar Mali ta saki manyan jami'an da aka kulle yayin juyin mulki
Gwamnatin rikon kwarya a Mali ta sanar da sakin wasu kusoshin siyasa da na Soji wadanda aka garkame a gidajen yari yayin juyin mulkin kasar na ranar 18 ga watan Agustan da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar ta bakin Assimi Goita da ke matsayin mataimakin shugaban kasa, kuma mafi kololuwar mukami bangaren Sojin da ke cikin gwamnatin hadakar, ya ce tun a yammacin jiya Laraba aka sakin mutanen 11 ciki har da tsohon Firaministan kasar Boubou Cisse.
Sauran fursunonin da aka saka har da tsohon kakain majalisar kasar Moussa Timbine da wasu janaral din soji 8, inda sharuddan sakin na su ya bayar da damar gurfanar da su gaban kotu idan bukatar hakan ta taso.
A litinin din makon nan ne, Gwamnatin rikon kwaryar ta Mali ta kammala haduwa, bayan da tun a watan jiya aka sanar da nadin shugaban kasa mataimakinsa da kuma Firaminista, ko da ya ke korafe-korafe sun dabaibaye gwamnatin musamman daga ketare kan yadda Soji suka mamaye mukamai a hadakar.
Sakin fursunonin ya biyo bayan bukatar kungiyar ECOWAS wadda ta nemi sakin ilahirin wadanda aka kame yayin juyin mulkin na watan Shekaran jiya da ya gudana ba tare da zub da jini ba.
Ecowas wadda ta mika bukatar bayan janyewa Malin takunkuman data kakaba mata a Talatar da ta gabata, ta kuma nemi wargaza hadakar Sojin kasar da suka bayyana kansu a matsayin jam’iyya mai rajin warware matsalar al’ummar kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu