An saki sojoji da 'yan siyasa da aka tsare yayin juyin mulki a Mali
Wallafawa ranar:
Gwamnatin rikon kwaryar Mali ta sanar da sakin yan siyasa da kuma sojojin da ake tsare da su bayan juyin mulkin kasar cikin su harda Firaminista Boubou Cisse.
Mataimakin shugaban kasar Assimi Goita ya bada sanarwar cewar an saki daukacin yan siyasar da sojojin da aka kama ranar 18 ga watan Agusta.
Rahotanni sun ce cikin wadanda aka sake harda shugaban Majalisar dokoki Moussa Timbine.
Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS ta cirewa Mali takunkumin karya tattalin arziki sakamakon gamsuwar da tayi na matakan da shugabannin kasar ke dauka na shirin mayar da gwamnati hannun farar hula.
A wani labarin kuma kasar Amurka ta sanar da dakatar da baiwa Mali taimakon soji har sai lokacin da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta gudanar da zabe, aka samu sabuwar gwamnati mai jagorancin kasar.
Jakadan Amurka a Yankin sahel J. Peter Pham yace zasu cigaba da baiwa kaasr Mali taimako ne kawai idan yanayi ya inganat a cikin kasar.
Yanzu dai haka an kafa gwamnatin rikon kwarya a Mali a karkashin Bah Ndaw wadda zata yi aiki na watanni 18.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu