Algeria-Nijar

Algeria ta sake kora dubban 'yan ci-rani zuwa Nijar

Wasu daga cikin 'yan ci-ranin da Algeria ta kora zuwa yankin Assamaka, da ke Jamhuriyar Nijar. 30/9/2020.
Wasu daga cikin 'yan ci-ranin da Algeria ta kora zuwa yankin Assamaka, da ke Jamhuriyar Nijar. 30/9/2020. © 2020 IOM Niger

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta  ce jami’an tsaron Algeria sun kame dubban ‘yan ci-rani gami da wasu dake neman mafaka a kasar, inda suka tilasta korarsu zuwa Jamhuriyar Nijar.

Talla

Cikin sanarwar da ta rabawa manema labarai a birnin Beirut, Human Rights Watch ta ce adadin ‘yan ci-ranin da Algeria ta kora ya zarta dubu 3 da 400.

Kungiyar ta kare hakkin dan adam ta kara da cewar Algeria na da ‘yancin kare iyakokinta, sai dai kama dubban ‘yan ci-rani, da kuma tsare su cikin hali na tagayyara duk da cewa akwai kananan yara ba tare da bin ka’idoji ba laifi ne babba.

Wani rahoton baya bayan nan da kungiyar ta Human Rights Watch ta fitar ya nuna cewa, a shekarar nan ta 2020 kadai, ‘yan ci-rani sama da dubu 16 Algeria ta kora zuwa Nijar, kamar yadda kungiyoyin bada agaji da ke ayyukan jin kai a kasar suka tabbatar.

Mafi akasarin bakin-hauren da Algerian ta kora kuma ‘yan Jamhuriyar Nijar ne, yayin da ragowar suka fito daga kasashe akalla 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.