Mali

AU ta janye dakatarwar da ta yi wa Mali

Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali Bah Ndaw, tare da mataimakinsa Kanal Assimi Goita a birnin Bamako.
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar kasar Mali Bah Ndaw, tare da mataimakinsa Kanal Assimi Goita a birnin Bamako. REUTERS

Kungiyar kasashen Afrika AU ta janye dakatarwar da ta yi wa Mali, matakin da ta dauka kan kasar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wa tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita a watan Agusta.

Talla

Matakin kungiyar ta AU dai ya zo ne bayan da kungiyar kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta sanar janye takunkuman da ta kakabawa kasar ta Mali, duk dai a dalilin juyin mulkin sojojin.

Takunkuman da aka janye kuwa sun hada da rufewa Malin iyakoki, da kuma haramta cinikayya da ita.

Kafin janyewa Mali takunkuman sai da gwamnatin rikon kwaryar kasar ta sanar da sakin wasu kusoshin siyasa da na soji wadanda aka garkame a gidajen yari yayin juyin mulkin kasar na ranar 18 ga watan Agustan da ya gabata.

Cikin sanarwar da gwamnatin ta fitar ta bakin Assimi Goita da ke matsayin mataimakin shugaban kasa, kuma mai mafi kololuwar mukami bangaren sojin da ke cikin gwamnatin hadakar, ya ce tdaga cikin fitattun mutanenda suka saki akwai tsohon Fira ministan kasar Boubou Cisse da tsohon kakin majalisar kasar Moussa Timbine da wasu Janar din soji 8.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI