Sudan

Yarjejeniyar sulhu tsakanin Sudan da 'yan tawaye za ta lashe dala biliyan 7

Ministan kudin Sudan Heba Mohammed Ali Ahmed, ya ce aiwatar da shirin yarjejeniyar sulhun da gwamnati ta cimma da ‘yan tawayen kasar zai lakume dala biliyan 7 da rabi.

Fira Ministan kasar Sudan Abdalla Hamdok yayin ganawa da manema labarai a birnin Khartoum.
Fira Ministan kasar Sudan Abdalla Hamdok yayin ganawa da manema labarai a birnin Khartoum. AP / File Photo
Talla

A karkashin yarjejeniyar sulhun da aka cimma da mayakan na ‘yan tawaye a ranar 3 ga watan Oktoban da muke, gwamnati ta sha alwashin sake gina yankunan kasar da yaki ya rusa, ciki harda yammacin yankin Darfur.

Tuni kuma Fira Minista Abdalla Hamdok ya amince da fara biyan dala miliyan 300 domin kaddamar da aikin sake gina sassan yankin Darfur da yaki ya daidaita.

Sai dai shirin aiwatar da yarjejeniyar na zuwa ne a daidai lokacin sabuwar gwamnati a Sudan din ke kokarin farfado da tattalin arzikin kasar daga durkushewa, bayan shafe tsawon lokaci yana cikin mawuyacin hali, sakamakon takunkuman karya tattalin arzikin da Amurka ta kakabawa tsohuwar gwamnatin Oumar Al-Bashir.

Matsalar tattalin arzikin kuma na daga cikin manyan dalilan da suka haddasawa tsohon shugaban fuskantar boren day a kai ga juyin mulkin da sojoji suka yi masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI