IMF-Afrika

Afrika na neman tallafin dala tiriliyan 1 don ceto tattalin arzikinta - IMF

Asusun bada Iamuni na duniya IMF, ya ce kasashen Afrika na bukatar akalla dala triliyan 1 da biliyan 200 nan da zuwa shekarar 2023, domin ceto tattalin arzikinsu da annobar coronavirus ta kassara.

Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva
Shugabar asusun bada lamuni na duniya IMF Kristalina Georgieva AFP/File
Talla

Sai dai yayin tsokaci a karshen makon nan, kan halin da tattalin arzikin kasashen na Afrika ke ciki, shugabar asusun na IMF Kristalina Georgieva, ta ce har yanzu ba a kai ga tara kashin farko na kason dala biliyan 345 daga cikin jumillar tallafin da nahiyar ta Afrika ke nema ba.

Rahoton bayan bayan nan da asusun bada lamunin na duniya ya fitar, ya yi hasashen cewar tattalin arzikin Afrika zai durkushe da kashi 2.5 saboda tasirin annobar coronavirus, daya daga cikin koma baya mafi muni da nahiyar ta gani a tarihi.

IMF ya kuma yi gargadin cewa, ko da yake tattalin arzikin kasashen na Afrika zai soma farfadowa daga shekara mai kamawa ta 2021, sai 2022 ake sa ran lamurra za su daidaita.

A cewar asusun, yanzu haka karin mutane miliyan 43 ke fuskantar barazanar fadawa cikin kangin talauci a Afrika, abinda zai shafe nasarar yaki da talaucin da aka cimma ta shekaru 5 a nahiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI