Jacob Zuma zai gurfana gaban Kotu kan rashawa

Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma.
Tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma. © AFP

Kotu a Afrika ta kudu ta bukaci tsohon shugaban kasar Jacob Zuma ya gurfana gaban kwamitin yaki da cin hanci da rashawa na musamman a wata mai kamawa don amsa tambayoyi kan zarge-zargen cin hanci da rashawa yayin mulkinsa na tsawon shekaru 9.

Talla

Jacob Zuma zai amsa tambayoyi ne gaban babban mataimakin alkalin alkalan kasar Raymond Zondo kuma shugaban kwamitin wanda aka kafa a 2018 don bincikar tsaffin ministoci da masu rike da madafun iko baya ga jami’an gwamnatin Zuma kan zarge-zargen karkatar da kudin da suka dabaibaye mulkinsa.

Zuma, wanda ya mulki Afrika ta kudu tun daga 2009 gabanin tilasta masa yin murabus a watan Fabarairun 2018 kwamitin wanda tarin manyan alkalai ke jagorancinsa ya bayyana cewa bayyanar tsohon shugaban gabansa na da muhimmanci don warware zarge-zarge da dama inda yanzu haka ake da shaidu akalla 34 da za su bayyana tare da Zuma gaban kwamitin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.