Sudan ta Kudu za ta sauya takardar kudinta

Wani dan Sudan ta Kudu dauke da kudin kasar na Fam a wajen babban bankinsu da ke birin Juba.
Wani dan Sudan ta Kudu dauke da kudin kasar na Fam a wajen babban bankinsu da ke birin Juba. Reuters

Majalisar zartaswar Sudan ta Kudu, ta cimma matsayar sauya takardar kudin kasar domin farfado da tattalin arzikinsu da ke cikin mawuyacin hali.

Talla

Ministan yada labaran Sudan ta Kudu Michael Makuei Lueth ne ya sanar da matakin gwamnatin kasar yayin ganawa da manema labarai a birnin Juba.

Sudan ta Kudu ta fara amfani da takardar kudinta na Fam ne a shekarar 2011, bayan ballewa daga kasar Sudan, da suka shafe shekaru da dama suna yakin basasa.

A watan Yulin da ya gabata babban bankin Sudan ta Kudun ya yi gargadin cewa kudaden kasashen wajen da ke baitulmalin kasar sun kare, abinda ya sa ba zai iya cigaba da kokarin ceto darajar kudin kasar na Fam daga faduwa ba.

Rahotanni sun ce mafi akasarin ‘yan Sudan ta Kudu sun gwammace ajiye kudadensu a gida, bisa fargabar cewa idan suka kai kudaden nasu ajiya a bankuna, gwamnati ka iya kwace su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI