Mali

'Yan ta'adda sun halaka 'yar mu bayan shafe shekaru 4 a hannunsu - Switzerland

Beatrice Stoeckli 'yan kasar Switzerland da mayaka masu ikirarin jihadi suka kashe a Mali
Beatrice Stoeckli 'yan kasar Switzerland da mayaka masu ikirarin jihadi suka kashe a Mali Ahmed Ouoaba/AFP

Ma’aikatar harkokin wajen Switzerland ta ce mayaka masu ikirarin jihadi sun halaka wata ‘yar kasar da suka yi garkuwa da ita a Mali.

Talla

Switzerland ta ce hukumomin Faransa ne suka bata tabbacin halaka matar mai suna Beatrice Stoeclkli wata guda da ya gabata.

Gwamnatin Switzerland ta dade tana fafutukar tattaunawa da mayakan masu ikirarin jihadi domin sakin Beatrice da suka sac eta shekaru 4 da suka gabata.

Ranar Alhamis da ta gabata, mayakan a Mali suka saki wasu fitattun mutane da suka dade suna garkuwa da su, da suka hada da jagoran ‘yan adawar kasar Souma’ila Cisse da kuma Sophie Petronin, wata ma’aikaciyar jinkai Bafaranshiya da ke aiki a kasar ta Mali, bayan shafe shekaru 4 a tsare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI