Najeriya

Najeriya: Buhari ya bada umurnin hukunta jami'an SARS

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Solacebase

Shugaban  Najeriya Muhammadu Buhari ya bada umurnin hukunta duk wani jami’in dan sandan da aka samu yana da hannu wajen aikata laifi, kwana guda bayan rusa rundunar yaki da ‘yan fashi da makami ta SARS.

Talla

Buhari yace rusa rundunar SARS shine mataki na farko na aiwatar da sauye sauye da gwamnatin sa ke yi na yiwa rundunar Yan Sandan gaba daya garambawul domin tabbatar da cewar jami’an tsaron Najeriya na gudanar da aikin kare rayuka da kuma dukiyoyin jama’a.

Shugaban wanda ya bayyana takaicinsa da rasa ran da aka samu wajen zanga zangar da aka yi a Jihar Oyo, ya ce ya bada umurnin gudanar da bincike domin gano abinda ya kai ga salwantar rai.

Daga karshe shugaban ya ce ya zama wajibi jama’a su san cewar a cikin rundunar Yan sandan akwai nagartattun jami’an dake aiki tukuru wajen kare lafiyar jama’a, saboda haka bai dace a bar tsirarun bata gari su bata musu suna ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.