Najeriya

Yawancin makarantun da aka bude a arewacin Najeriya ba su cika ka'idojin kariya daga Coronavirus ba

A Nigeria yau wasu jihohi arewacin kasar ke bude makarantu bayan sama da watanni 7 a rufe sakamakon cutar Coronavirus, sai dai kamar yadda zaku ji a wannan rahoton da Shehu Saulawa ya aiko mana,rashin cika wasu ka’idojin da aka shimfida,ya shafi yawan yaran da suka koma aji yau.

Yara 'yan makaranta a Maiduguri, Najeriya.
Yara 'yan makaranta a Maiduguri, Najeriya. Thomson Reuters Foundation/Kieran Guilbert