Kamaru

MDD ta yi wa Kamaru kashedi kan Kamto

Madugun ‘yan adawan Kamaru Maurice Kamto ya ce, hukumomin kasar na ci gaba da yi masa daurin talala a gidansa duk da cewa Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci a gaggauta sakin sa.

Maurice Kamto ya fafata da shugaba Paul Biya a zaben 2018, amma bai samu nasara ba.
Maurice Kamto ya fafata da shugaba Paul Biya a zaben 2018, amma bai samu nasara ba. REUTERS/Zohra Bensemra
Talla

An yi wa Kamto daurin talala ne bayan ya kira wata zanga-zangar lumana ta nuna adawa da shugaba Paul Biya da ya shafe gomman shekaru yana mulkar Kamaru, yayin da Jami’an Kare Hakkin Bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya suka bukaci sakin sa tare da mukarrabansa da aka kama a ranar 22 ga watan Satumba.

Kamto dai shi ne babban dan adawan shugaba Biya wanda ya kwashe shekaru 38 yana mulkar kasar.

Madugun ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, har yanzu jami’an ‘yan sanda na ci gaba da zaman dirshen a kofar gidansa, kuma sun yi amfani da motarsu wajen toshe hanyar ficewa.

Sai dai sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta ce, matakin tsare Kamto ka iya zama take hakkinsa da kuma ‘yancinsa na gudanar da zanga-zangar lumana.

Hukumomin Kamaru sun ki cewa uffam bayan Kamfanin Dillancin Labaran Faransa ya tuntube su don jin ta bakinsu.

Lauyoyin Kamto sun ce, sun maka gwamnatin kasar a kotu domin kalubalantar matakin yi masa daurin talala, kuma nan kusa za a fara zaman sauraren shari’a a cewarsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI