Sudan-MDD

Mutane miliyan 9 na bukatar agajin abinci cikin gaggawa a Sudan- MDD

Wasu al'ummar Sudan.
Wasu al'ummar Sudan. AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 9 ke bukatar agajin abincin gaggawa a kasar Sudan sakamakon illar da ambaliyar ruwan sama ta haifar a kasar.

Talla

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta gabatar da wannan adadi mai tayar da hankali, wanda ke nuna cewar illar da ambaliyar ta yi ya zarce abinda aka yi hasashe a baya.

Hukumar ta ce ambaliyar ta mamaye daruruwan gonaki da rusa gidaje da kuma asarar rayuka, abinda ya sa aka yi kididdigar da ta nuna cewar mutane sama da miliyan 9 na bukatar agajin abinda za su ci.

Kasar Sudan ta dade tana fama da matsalar ambaliya amma cikin fiye da shekaru 100 ba ta ga irin ambaliyar bana ba, wanda ya sanya mutane da dama suka tagayyara.

Hukumar samar da abincin ta ce anyi asarar kayan abincin da ya kai tan miliyan guda, yayin da ake fargabar barkewar cututtuka saboda gurbacewar ruwan sha.

Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ana fama da matsalar kudaden da za a yi amfani da su wajen tallafawa jama’ar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.