IMF da Bankin Duniya sun bakaci tallafawa kasashe matalauta saboda korona

Logon cibiyar Asusun IMF dake Washington na kasar Amurka
Logon cibiyar Asusun IMF dake Washington na kasar Amurka REUTERS/Yuri Gripas/File Photo

Asusun bada lamuni Duniya IMF tare da Bankin Duniya sun sabunta kira ga ma’azurtan kasashe kan su tallafawa matalautan kasashe don su samu damar tunkarar illolin da Coronavirus ta haifarwa tattalin arzikinsu.

Talla

Yayin taron hadin gwiwa na shekara-shekara da manyan ma’aikatun kudin na Duniya 2 suka gudanar ranar Laraba, sun ce wajibi ne kasashe su mike tsaye wajen zuba kudade a bangarorin da ke fuskantar barazanar rushewa sakamakon yadda annobar Covid-19 ta kassara su.

Acewar ma’aikatun biyu har sai ma’azurtan kasashen sun kawar da kai daga asarar da su kansu cutar ta haddasa musu tare da tallafawa kasuwanci da ma’aikatun da ke barazanar durkushewa saboda annobar ba kadai a kasashen ba, shi ne za a iya farfadowa daga matsalar tattalin arzikin Duniya baki daya ke shirin tsunduma.

Shugabar IMF Kristalina Geaorgieva da takwaranta na bankin Duniya David Malpass sun sabunta kiran ga manyan kasashen ciki har da China wajen ganin sun sassauta wajen karbar basukan da suke bin matalautan kasashe don basu damar murmurowa daga illar da annobar ta corona ta yi musu.

Da ta ke zantawa da manema labarai, Georgieva a tsawon watanni 9 da Duniya ta yi ta na fuskantar wannan annoba, galibin matalautan kasashen a kowacce rana na fuskantar koma baya ne, wanda ke nuna basu da karfin tunkrar matsalolinsu bare su koma fagen biyan basukan da ek aknsu.

Shi kuwa David Malpass cewa ya yi duk da hasashen farfadowar tattalin arziki a 2021 Duniya za ta fuskanci asarar akalla dala Tiriliyan 12 wanda kuma zai fi shafar matalautan kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI