Jami'an tsaron Uganda sunyi kaca-kaca da ofishin Bobi Wine

An saki shahararren mawakin nan da ya rikede zuwa dan siyasa a kasar Uganda, Bobi Wine, bayan da jami'an tsaron kasar suka tsare shi yayin wani samame da suka kai ofisoshinsa a Kampala babban birnin kasar.

Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine
Mawaki, dan majalisa kuma dan takarar Uganda Bobi Wine France24
Talla

Robert Kyagulanyi da aka fi sanani da Bobi Wine, yanzu haka dan majalisar dokokokin kasar Uganda ne daga jam’iyyar adawa ta NUP, kuma ba karon farko ba kenan ake tsare shi, sakamakon bayyananniyar adawarsa da Shugaba Yoweri Museveni, wanda ke mulkin kasar ta gabashin Afirka tun a shekarar 1986.

Lauyan Wine, Anthony Wameli ya ce an kame wanda yake karewa ne a ranar Laraba, bayan da sojoji da ‘yan sanda suka mamaye a ofisoshin jam’iyyarsa ta adawa, National Unity Platform, wanda yake neman shugabancin kasar a karkashinta tare da katse hanyoyin da ke isa ofishin, kafin awon gaba da shi da wasu jigajigan jam’iyyar.

Lauyan, wanda yace ba’a bayyana musu dalilin samamenba, yace matakin abin Allah wadai ne, kuma karan tsaye ne ga dimokiradiyya.

Tun a safiyar ranar Laraban, ficececen mawakin da ya rike de zuwa dan siyasa mai adawa da gwamnti, ya wallafa a shafinsa na Tweeter cewa 'yan sanda da sojoji sun "kutsa kai cikin ofisoshin tare da kwashe muhimman takardu, bayan raunata wasu magoya bayansa.

Kakakin 'yan sandan Uganda, Patrick Onyango ya tabbatar da cewa "sun kai samame ofishin NUP, domin gudanar bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI