Kabore ya bukaci dawowar Blaise Compaore Burkina Faso daga gudun hijira
Wallafawa ranar:
Shugaban Kasar Burkina Faso Christian Mark Kabore ya ce hambararen shugaban kasar Blaise Compaore na iya komawa gida daga inda ya samu mafakar siyasa bayan kifar da gwamnatinsa.
A hira ta musamman da ya yi da RFI da kuma tashar talabijin din France 24, shugaba Kabore a karon farko ya ce ya na tunanin ganin tsohon shugaban ya koma gida tun bayan barin kasar a shekarar 2014.
Kabore ya ce muddin ya samu nasarar zaben da za a yi ranar 22 ga watan Nuwamba zai kaddamar da shirin sasanta al’ummar kasar wadda za ta bai wa Compaore damar komawa a farkon watanni 6 na shekarar 2021.
Kasar Burkina Faso ta dade tana fama da rikicin 'yan bindiga wanda ya hana jama’ar kasar kwanciyar hankali.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu