An soma yakin neman zaben shugabancin Cote d'Ivoire mai cike da rudani

Alhamis din nan ake soma yakin neman zaben neman shugabancin Ivory Coast a hukumance, inda shugaba mai cike Alassane Ouattara ke neman wa’adi na uku mai cike da cece-kuce, yayin da jam’iyyun adawa ke kokarin kauracewa zaben da kuma bijirewa doka, lamarin da ke haifar da fargabar tashin hankali.

Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alasane Outtara
Shugaban kasar Cote d'Ivoire Alasane Outtara REUTERS/Luc Gnago
Talla

Masu lura da al'amura na fargabar zaben na ranar 31 ga watan nan na Oktoba ka iya haifar da rikici, makaimaicin wanda aka gani tsakanin 2010 -2011, inda kimanin mutane dubu 3 suka rasa rayukansu.

Ko a karshen makon da ya gabata saida gungun jam’iyyun adawa a Ivory Coast suka gudanar da zanga-zanga a birnin Abijan, domin jadda da adawa da matakin shugaba Outtara na neman tazarce a wa’adi na uku, wanda ya samu halartan dubbun magoya baya.

Mutane hudu ke takaran neman shuganacin kasar yanzu haka, da suka hada da shugaban mai ci Alasane Ouattara mai shekaru 78; da Tsohon shugaban kasa Henri Konan Bedie mai shekaru 86; da tsohon firaminista Pascal Affi N'Guessan sai kuma tsohon dan majalisa Kouadio Konan Bertin.

Kutun fasalta tsarin mulkin kasar ta ki amincewa da takarar wasu mutane 40 ciki har da tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo, mai shekara 75, da kuma tsohon jagoran ‘yan tawaye da shugaban majalisa Guillaume Soro, mai shekaru 47, wadanda suka taka rawa a rikicin da ya dabaibaye kasar bayan rigingimun zabe a 2010, wanda yayi sanadiyar hallaka sama da mutane dubu 3.

Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya (ICC) da ke Hague ta saki Gbagbo da sharadi bayan an wanke shi a watan Janairun 2019 daga laifukan cin zarafin bil'adama a lokacin rikicin.

Yanzu haka yana Brussels yayin da ake jiran sakamakon daukaka karar da aka yi kan hukuncin na ICC.

'Yan adawar kasar dai sun koka kan yunkurin Ouattara na sake darewa kan karagar mulki a wa'adi na uku duk da cewa kundin tsarin mulki ya takaita wa'adi biyu kachal.

Bayan sake zabensa a 2015, Ouattara ya sanar a watan Maris cewa ba zai nemi wa’adi na uku ba, amma ya canza shawara bayan mutuwar bazatan magajinsa, Firayinminista Amadou Gon Coulibaly, a watan Yuli sakamakon bugun zuciya.

Shugaba Ouattara da magoya bayansa sun yi ikirarin cewa sake fasalin kundin tsarin mulkin kasar na shekarar 2016 ya share wa’adin mulkinsa da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI