Guinea

'Yan takarar shugabancin Guinea na gangamin karshe gabanin zaben karshen mako

'Yan takaran zaben shugaban kasar Guinea da za a yi a karshen wannan mako sun ci gaba da yakin neman goyan bayan jama’a alhamis din nan, inda birnin Conakry ya ga cincirindon jama’ar da aka dade ba a gani ba.

Wasu masu gangami a Guinea Conakry.
Wasu masu gangami a Guinea Conakry. REUTERS/Saliou Samb NO RESALES
Talla

Daruruwan magoya bayan shugaba Alpha Conde da ke neman wa’adi na 3 suka cika titunan birnin Conakry a cikin motocin su wadanda ke bushe bushe da amfani da jiniya domin nuna goyan bayan su ga shugaba Alpha Conde mai shekaru 82.

Bayan kwashe makwanni yana zagaya biranen kasar, shugaba Conde da ke fafatawa da wasu Yan takara 11 ya bukaci al’ummar kasar da su sake bashi goyan baya domin cigaba da ayyukan raya kasar da ya sa a gaba.

Tuni wannan bukata ta shi ta gamu da suka daga Yan adawar kasar, tun bayan lokacin da ya sauya kundin tsarin mulki, abinda ya haifar da zanga zanga da kuma tashin hankali.

Shima babban shugaban yan adawa Cellou Dalein Diallo ya koma Conakry daga kasashen waje inda daruruwan magoya bayan sa sanye da kayan dake nuna alamar jam’iyar sa suka tarbe shi.

Diallo wanda tsohon Firaminista ne lokacin mulkin Lansana Conte na daga cikin wadanda zasu sake fafatawa da Conde a zaben na ranar lahadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI